Zaben Najeriya na 2023
babban zaben da aka gudanar a Najeriya / From Wikipedia, the free encyclopedia
An gudanar da babban zaɓe a Najeriya ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 domin zaɓar shugaban ƙasa da mataimakin shugaban ƙasa da ƴan majalisar dattawa da na wakilai. Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari mai ci ya cika iyaka kuma ba zai iya sake neman tazarce a karo na uku ba.[1] Ana kallon wannan zaɓe a matsayin mafi tsauri tun bayan kawo karshen mulkin soja a shekarar 1999.[2]