Mohamed Bazoum
From Wikipedia, the free encyclopedia
Mohamed Bazoum (an haifi Bazoom ranar 3 ga watan Janairu shekara ta alif ɗari tara da hamsin da tara 1959) Ɗan siyasar Jamhuriyar Nijer, kuma tsohon Shugaban Ƙasar Nijar. Bazoum Balarabe ne ɗan asalin Jamhuriyar Nijar wanda ya kasance Shugaban Jam’iyyar (PNDS- Ta Tarayya) tun daga shekarar 2011, Ya Kuma yi aiki a gwamnatin Nijar a matsayin Ministan Harkokin Waje daga shekara ta 1995 zuwa shekara ta 1996 da kuma sake zama Ministan daga shekara ta 2011 zuwa shekara ta 2015. Ya kasance ƙaramin minista a fadar shugaban ƙasa daga shekara ta 2015 zuwa shekarar 2016. Sannan Kuma ya kasance ƙaramin ministan cikin gida tsakanin shekarar 2016 zuwa 2020, lokacin da ya yi murabus don mayar da hankali kan tsayawa takarar shugabancin ƙasar a shekarar 2020. Inda yayi Nasarar lashe zaɓen da kaso 55.67% cikin ɗari.[1]
Mohamed Bazoum | |||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
2 ga Afirilu, 2021 - 26 ga Yuli, 2023 ← Mahamadou Issoufou
21 ga Afirilu, 2011 - 2015 ← Aminatou Maiga Touré - Aïchatou Boulama Kané →
1993 - 2021
| |||||||||
Rayuwa | |||||||||
Haihuwa | Bilabrin (en) , 1 ga Janairu, 1960 (64 shekaru) | ||||||||
ƙasa | Nijar | ||||||||
Ƙabila | Larabawan Diffa | ||||||||
Karatu | |||||||||
Makaranta |
Université Cheikh Anta Diop (en) (1979 - 1984) : Falsafa | ||||||||
Harsuna | Faransanci | ||||||||
Sana'a | |||||||||
Sana'a | ɗan siyasa, international forum participant (en) da Malami | ||||||||
Mahalarcin
| |||||||||
Kyaututtuka | |||||||||
Imani | |||||||||
Addini | Mabiya Sunnah | ||||||||
Jam'iyar siyasa | Nigerien Party for Democracy and Socialism |