jiha a Najeriya / From Wikipedia, the free encyclopedia
Jihar Kaduna wace Ake mata kirari da (Cibiyar Ilimi), ta samu wannan sunan ne a Allah ya azurta ta da makarantu na Ilimi, Kaduna jiha ce dake a Arewacin Najeriya. Babbar cibiyar birnin Jihar na da suna Kaduna, wanda ta kasance birni ta 8 mafi girma daga cikin biranen ƙasar Najeriya. Kamar yadda yake dangane a ƙiyasin shekara ta 2006. An ƙirƙiri Jihar Kaduna shekara 7 bayan samun ƴancin kai, an ƙirƙire ta a shekarar 1967, da sunan Jihar Tsakiyar Arewa, wadda kuma ta haɗa da Jihar Katsina ta yanzu, Kaduna ta samu iyakar ta ne a shekarar 1987. Kaduna Ita ce jiha ta uku mafi girman ƙasa kuma ta haɗa da yawan mutane daga cikin sauran Jihohin Najeria, ana kuma ma Jihar Kaduna laƙabi ko kirari da Cibiyan koyon Ilimi (Centre of Learning,) saboda ta kasance tana da manyan makarantu na gaba da sakandare masu muhimmanci, kamar su Jami'ar Ahmadu Bello, Jami'ar Tsaro ta Najeriya da dai sauran su.[1][2]