Hausawa
kabila a Yammancin Afirka / From Wikipedia, the free encyclopedia
Hausa (Sunan mutum ɗaya a jinsin mace da namiji: Bahaushe بَهَوْشٜىٰ (N), Bahaushiya بَهَوْشِيَا (M); Jami'i: Hausawa هَوْسَاوَا da kuma mai gaba ɗaya wato sunan harshen: Hausa;[1] Ajami: مُتَنٜىٰنْ هَوْسَا) al'umma ce dake zaune a arewa maso yammacin tarayyar Nijeriya. Da kudu maso yammacin jamhuriyyar Nijar. Al'umma ce mai ɗimbin yawa, sun bazu a cikin ƙasashen Afirka,[2][3] da kasashen Larabawa, kuma a al'adance masu matuƙar hazaƙa ne, aƙalla akwai sama da mutane miliyan hamsin waɗanda harshen Hausa shi ne asalin harshensu. A tarihi ƙabilar Hausawa na tattare a salsalar birane wato alƙarya. Hausawa dai sun sami kafa daularsu ne tun daga shekarun 1300's, sa'adda suka sami nasarori da dauloli kamar su daular Mali, Songhai, Borno, da kuma Fulani, a ƙarni na 19 Hausawa suna amfani da Kuma Doki ne domin yin sufuri da balaguro.[4] Mutane kimanin sama da Kuma miliyan 50 ne ke magana da harshen Hausa a Najeriya da Nijar da Arewacin Ghana da kuma wasu al’umma daga yankin Kaolack a senigal har zuwa khartum dake ƙasar Sudan, Asalin inda zuri'ar Hausawa take shi ne Kano da Katsina da kuma Sokoto.[5] Asalin Hausawa maguzawa ne, amma sun shafe daruruwan shekaru da karɓar addinin musulunci ƙarkashin mulkin sarakunan Haɓe, wanda suka daina yin bori da tsubbace-tsubbace, zuwan Shehu Usman dan Fodio ne yasa ya kawar da mulkin waɗannan sarakunan na ƙasar Hausa, ta hanyar yaƙar Hausawa da sarakunansu na haɓe a Gobir, Zazzau da wasu yankunan ƙasar Hausa. Wanda wannan juyin mulkin ne yasa Shehu Usman ɗan Fodio ya kafa Daular Fulani a Hausa Fulani a ƙasar Hausa, kuma hakan yasa masarautun Ƙasar Hausa sun kasance a ƙungiyar tuta ɗaya ta Usman dan Fodio.[6] Hausawa suna kiran al’adunsu da al’adun gargajiya, wacce suke yi duk shekara, ko a talabijin ko Bidiyo, ko kuma aikace cikin al’amuran yau da kullum.[7] Na daga cikin rubutun Hausawa, suna yin rubutu ne asali da Ajami, rubutu ne da haruffan larabci amman a luggar Hausa, kuma suna rubutawa ne a fallen takarda.[8]
| |
Jimlar yawan jama'a | |
---|---|
40,000,000 | |
Yankuna masu yawan jama'a | |
Ivory Coast, Togo, Benin, Burkina Faso, Kameru, Najeriya, Nijar, Sudan, Cadi, Mali, Senegal, Gabon, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Jamhuriyar Kwango, Gini Ikwatoriya, Guinea-Bissau, Gambiya, Ghana, Habasha, Eritrea da Aljeriya |