Canjin yanayi a Argentina
From Wikipedia, the free encyclopedia
Ana hasashen canjin yanayi zaiyi tasiri sosai kan yanayin rayuwa a Argentina.:30Yanayin Argentina yana canzawa dangane da yanayin hazo da yanayin zafi. Mafi girman haɓakar hazo (daga lokacin 1960-2010)ya faru a sassan gabashin ƙasar. Haɓɓakar hazo ya haifar da samun sauye-sauyen hazo daga shekara zuwa shekara a sassan arewacin ƙasar, tare da ƙarin haɗarin daɗaɗɗen fari, wanda ke damun noma a waɗannan yankuna.
Kodayake yanayin zafi ya ƙaru a hankali fiye da matsakaicin duniya, dukda haka waɗannan tasirin sun faru a wurare da yawa. Yanayin zafi mafi girma na iya rage dusar ƙanƙara ta hunturu,wanda ke haifar da raguwar kwararar kogi (ƙarancin ruwa), wanda zai iya rage samar da wutar lantarki; an lura da asarar har zuwa 40%. Idan waɗannan yanayin sun cigaba, anyi hasashen cewa canjin yanayi zai ƙara muni da bala'o'in dake akwai kamar ƙara ƙarfin da yawan ambaliyar ruwa ko ƙirƙirar sabbin.