Yaƙi
Faɗa tsakanin ɓangarori guda biyu / From Wikipedia, the free encyclopedia
Yaki babban rikici ne na makami [2] tsakanin jihohi, gwamnatoci, al'ummomi, ko ƙungiyoyin sa-kai kamar 'yan amshin shata, ƴan tawaye, da kuma 'yan bindiga. Gabaɗaya ana siffanta shi da matsananciyar tashin hankali, halaka, da mace-mace, ta amfani da dakarun soji na yau da kullum ko ba na yau da kullum ba. Yaƙi yana nufin ayyuka gama-gari da halayen nau'ikan yaƙi, ko na yaƙe-yaƙe gabaɗaya. Gaba ɗaya yaƙin ne wanda ba'a keɓance shi ga halaltaccen hari na soji ba, kuma zai iya haifar da gaggarumin wahala da hasarar rayukan fararen hula ko sauran waɗanda ba na yaƙi ba.[3]
yaƙi | |
---|---|
type of conflict (en) | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | armed conflict (en) , social issue (en) , aukuwa, military activity (en) da group conflict (en) |
Associated hazard (en) | casualty (en) , war damage (en) da uncertainty (en) |
Has cause (en) | casus belli (en) da conflict escalation (en) |
Yana haddasa | effects of war (en) |
Karatun ta | military history (en) , war studies (en) , peace and conflict studies (en) , Institute for the Study of War (en) da sociology of peace, war, and social conflict (en) |
Hashtag (en) | wars |
Has characteristic (en) | type of war (en) |
Gudanarwan | Jarumi |
Handled, mitigated, or managed by (en) | preventive diplomacy (en) , peacebuilding (en) da anti-war movement (en) |
Hannun riga da | zaman lafiya |
Yayin da wasu masana binciken yaki suka yi la'akari da yaki a matsayin yanayin duniya da kakanni na dabi'ar mutum, wasu kuma suna jayayya cewa yana da nasaba da takamaiman al'adun zamantakewa, tattalin arziki ko yanayin muhalli. [4]