Wurare Mafiya Tsarki a Musulunci
From Wikipedia, the free encyclopedia
Wurare Mafiya Tsarki a Musulunci sune waɗanda aka ambata ko akayi maganar su a cikin Alqur'ani, cewa suna ɗauke da alfarma mai muhimmanci a Musulunci. Makka [1] da Madina [2] [3] [4] a Ƙasar Saudi Arabiya su ne birane biyu mafiya tsada a cikin Islama, an yi tarayya a tsakanin dukkan mazhabobi. A cikin hadishin Islama, da Kaaba a cikin Makka ke zama waje mafi tsarki sai mai biye mata shine Masallacin Annabi a Madina, da kuma Al-Aqsa a Urushalima. Akwai wurare masu tsarki waɗanda suke a cikin Makka ; Mina, Arafat, da Muzdalifah . [5]
Wurare Mafiya Tsarki a Musulunci | |
---|---|
jerin maƙaloli na Wikimedia | |
Bayanai | |
Addini | Musulunci |
Anfi ittifaƙi akan cewa wuraren ibada mafiya tsarki a Musulunci guda huɗu ne ciki harda masallacin Umayyah dake a Damascus, sannan da babban masallacin Kairouan a Kairouan, [6] [7] [8] da Sanctuary Ibrahim a Hebron, Bukhara, [9] [10] Eyüp a Kasar Istanbul, [11] [12] da Harar . [13] [14]