Tsohon Birnin Damascus (Larabci: دِمَشْق ٱلْقَدِيمَة, romanized: Dimašq al-Qadīmah) birni ne mai tarihi na Damascus, Siriya. Tsohon birnin wanda yana daya daga cikin tsofaffin biranen da ake cigaba da zama a duniya,[1] ya kunshi wuraren binciken kayan tarihi da dama da suka hada da wasu majami'u da masallatai na tarihi. Al'adu da yawa sun bar tarihi, musamman na Hellenistic, Roman, Byzantine da Musulunci. A cikin 1979, cibiyar tarihi na birnin, wanda ke kewaye da ganuwar zamanin Roman, UNESCO ta ayyana shi a matsayin Gidan Tarihi na Duniya. A cikin watan Yunin 2013, UNESCO ta sanya dukkan wuraren Siriya a cikin jerin abubuwan tarihi na duniya da ke cikin haɗari don yin gargadi game da haɗarin da ke tattare da su saboda yakin basasar Siriya.[2]