Sviatoslav I
From Wikipedia, the free encyclopedia
Sviatoslav ko kuma Svyatoslav I Igorevich (Template:Lang-orv;[lower-alpha 1] c. 943 – 972) ya kasance yariman Kiev daga 945 har zuwa mutuwar shi a 972.[1] Ya yi fice da jajircewarsa na kamfe a gabas da kudu, wanda ya janyo rushewar manyan Kasashen Iko guda biyu na Turai, Khazaria da kuma Daukar Bulgaria ta Farko. Ya mamaye yarukan Gashin Slavic, yayi nasara akan Alans kuma ya farmaki Volga Bulgars,[2] kuma a wasu lokutan ya hada gwiwa tare da Pechenegs da kuma Magyars (mutanen Hungariya).
Sviatoslav I | |||||
---|---|---|---|---|---|
945 - 972 ← Igor of Kiev (en) - Yaropolk I of Kiev (en) →
945 - 969 ← Igor of Kiev (en) - Vladimir the Great (en) → | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Kiev, 942 | ||||
ƙasa | Kievan Rus' (en) | ||||
Mutuwa | Dnieper Rapids (en) , 972 | ||||
Yanayin mutuwa | kisan kai | ||||
Ƴan uwa | |||||
Mahaifi | Igor of Kiev | ||||
Mahaifiya | Olga of Kiev | ||||
Abokiyar zama | Predslava (en) | ||||
Ma'aurata | Malusha of Dereva (en) | ||||
Yara | |||||
Yare | Rurik dynasty (en) | ||||
Karatu | |||||
Harsuna | Old East Slavic (en) | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | Mai wanzar da zaman lafiya da ɗan siyasa | ||||
Imani | |||||
Addini | Slavic religion (en) |
[3][4][5][6] Bayan rasuwar mahaifinsa Igor a 945, mahaifiyar Sviatoslav Olga ta yi mulki a matsayin mai rikon kwarya na Kiev har zuwa 962. [1] [2] [3] Sarautarsa ta tsawon shekaru goma a kan Kievan Rus' ta kasance alama ce ta fadada cikin kwarin Kogin Volga, da tsaunukan Pontic, da Balkans, wanda ya kai shi ga sassaƙa wa kansa babbar jiha a Turai. [7][8] shekara ta 969, ya koma kujerarsa zuwa Pereyaslavets a kan Danube. [1] [2] [9][10] A 970, ya nada 'ya'yansa maza Yaropolk da Oleg a matsayin sarakuna na Kiev da Drelinia, yayin da ya nada Vladimir, ɗansa wanda mai masa hidima a gidansa kuma bawansa Malusha, a matsayin yarima na Novgorod.
Dangane da sauya addinin mahaifiyar sa zuwa Kiristanci, Sviatoslav ya cigaba da bauta a matsayin mara addini na tsawon rayuwarsa.[3] A sanadiyar mutuwarsa na ba zato ta harin kwanton bauna, ba’a samu daman hade garuruwan sa da ya mamaye ba a matsayin daula guda, haka zalika a dalilin rashin samar da tsayayyen magaji ya janyo matsanancin rikici a tsakanin ‘ya’yan sa, wanda ya janyo mutuwar Yaropolk da Oleg, a yayin da Vladimir ya zamo sarki.[4]