Navi Pillay
From Wikipedia, the free encyclopedia
Navanethem "Navi" Pillay (an haife ta ranar 23 ga watan Satumba shekara ta 1941) ƙwararriyar masaniyaf shari'a ce ta Afirka ta Kudu wanda ta yi aiki a matsayin Babbar Kwamishinan Kare Haƙƙin Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya daga 2008 zuwa 2014.'Yar Afirka ta Kudu 'yar asalin Tamil ta Indiya, ita ce mace ta farko da ba farar fata ba a Kotun Koli ta Afirka ta Kudu,[1] kuma ta yi aiki a matsayin alkaliya ta Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya da Shugabar Kotun Hukunta Laifukan Ruwanda. .Wa'adinta na shekaru huɗu a matsayin Babban Kwamishinan a hukumar kare Ƴancin Ɗan Adam ya fara a ranar 1 ga Satumba 2008[2] kuma an ƙara ƙarin shekaru biyu a 2012.[3] Yarima Zeid bin Ra'ad ne ya gaje ta a watan Satumban 2014.A cikin Afrilun shekarar 2015 Pillay ta zama Kwamishina ta 16 na Hukumar Yaƙi da Hukuncin Kisa ta Duniya. Har ila yau, tana ɗaya daga cikin manyan mutane 25 a hukumar yaɗa labarai da dimokuraɗiyya da ƙungiyar masu rajin kare hakkin bil'adama ta Reporters Without Borders ta kaddamar.[4]
Navi Pillay | |||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|
ga Afirilu, 2015 -
1 Satumba 2008 - 31 ga Augusta, 2014
11 ga Maris, 2003 - 31 ga Augusta, 2008 | |||||||
Rayuwa | |||||||
Haihuwa | Durban, 23 Satumba 1941 (82 shekaru) | ||||||
ƙasa | Afirka ta kudu | ||||||
Karatu | |||||||
Makaranta |
University of Natal (en) Harvard Law School (en) | ||||||
Matakin karatu | doctorate (en) | ||||||
Harsuna | Turanci | ||||||
Sana'a | |||||||
Sana'a | mai shari'a da Lauya | ||||||
Mahalarcin
| |||||||
Employers | Majalisar Ɗinkin Duniya | ||||||
Kyaututtuka | |||||||
Mamba | Permanent United Nations Fact Finding Mission on the Israel Palestine conflict (en) |