Mohammed bin Rashid Al Maktoum
Sarkin Dubai / From Wikipedia, the free encyclopedia
Sheikh Mohammed bin Rashid Al Maktoum GBE Larabci: محمد بن راشد آل مكتوم; Muḥammad bin Rāshid al Maktūm; an haife shi 15 Yuli 1949) shi ne Mataimakin Shugaban ƙasa da Firayim Minista na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), kuma mai mulkin Masarautar Dubai.
Mohammed bin Rashid Al Maktoum | |||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
13 Mayu 2022 - 14 Mayu 2022 ← Khalifa bin Zayed Al Nahyan - Mohammed bin Zayed Al Nahyan →
11 ga Faburairu, 2006 - ← Maktoum bin Rashid Al Maktoum (en)
5 ga Janairu, 2006 -
4 ga Janairu, 2006 - ← Maktoum bin Rashid Al Maktoum (en)
9 Disamba 1971 - | |||||||||||
Rayuwa | |||||||||||
Haihuwa | Dubai (birni), 15 ga Yuli, 1949 (74 shekaru) | ||||||||||
ƙasa | Taraiyar larabawa | ||||||||||
Ƴan uwa | |||||||||||
Mahaifi | Rashid bin Saeed Al Maktoum | ||||||||||
Abokiyar zama |
Hind bint Maktoum bin Juma Al-Maktoum (en) Houria Ahmed Lamara (en) Princess Haya bint Al-Hussein of Jordan (en) (10 ga Afirilu, 2004 - 7 ga Faburairu, 2019) | ||||||||||
Yara |
view
| ||||||||||
Ahali | Maktoum bin Rashid Al Maktoum (en) , Hamdan bin Rashid Al Maktoum (en) da Ahmed bin Rashid Al Maktoum (en) | ||||||||||
Yare |
Al Maktoum (en) House of Al-Falasi (en) | ||||||||||
Karatu | |||||||||||
Makaranta | Mons Officer Cadet School (en) | ||||||||||
Harsuna |
Larabci Turanci | ||||||||||
Sana'a | |||||||||||
Sana'a | ɗan siyasa, ɗan kasuwa da maiwaƙe | ||||||||||
Mahalarcin
| |||||||||||
Kyaututtuka | |||||||||||
Imani | |||||||||||
Addini | Mabiya Sunnah | ||||||||||
IMDb | nm4549876 | ||||||||||
sheikhmohammed.ae |
Shi ne mutumin da ya haɓaka Dubai ta zama birni na duniya, [1] da kuma ƙaddamar da wasu manyan kamfanoni ciki har da kamfanin jiragen sama na Emirates Airline, DP World, da Jumeirah Group. Yawancin waɗannan ana riƙe su ne ta hanyar Dubai Holding, kamfani tare da kamfanoni iri-iri da saka jari. Sheikh Mohammed ya kula da ci gaban ayyuka da dama a cikin Dubai wadanda suka hada da kirkirar filin shakatawa na fasaha da kuma yankin tattalin arziki na kyauta, Dubai Internet City, Dubai Media City, Cibiyar Kudi ta Duniya ta Dubai, Tsibiran Palm da otal din Burj Al Arab. Ya kuma jagoranci gina Burj Khalifa, gini mafi tsayi a duniya.