Kwaɗo
From Wikipedia, the free encyclopedia
Kwado wani halitta ne Wanda Allah ya halitta cikin halittu masu tsalle Yana da kafa huɗu. Wasu nacin naman kwaɗo, sannan kwado iri-iri ne, sannan ba kowane ake ci ba domin Yana da dafi sosai. Cin kwado al'ada ce ta mutane daban-daban kamar yadda ba kowa ke iya ci ba. Mu dauki Najeriya a matsayin misali; A arewacin Najeriya cin kwado kazanta ne a al'adan mutanen yankin wanda mafi yawansu Hausawa ne kuma musulmi duk kuwa da kasancewarsa Halas ne a addininsu na [[musulunci]]. Amma a Kudancin Najeriya nama ne mai tsafta da dafi domin al'adarsu ta tafi a kan hakan.