Komfuta
From Wikipedia, the free encyclopedia
Kwamfuta na’ura ce mai aiki da wutan lantarki, da ƙwaƙwalwa, wajen karɓa da sarrafawa da adanawa da kuma miƙa bayanai, a sigogi daban-daban. Wannan shine ta’arifin kwamfuta a takaice. Bayan haka kwamfuta na tattare ne da manyan ɓangarori guda biyu; ɓangaren gangan jiki, wanda aka fi sani da Hardware, a turance. Sai kuma ɓangaren ruhi ko rai, wanda ake kira Software (manhaja), shima a turance. Kafin mu yi nisa, mai karatu zai ji ana fassara kalmomin turancin nan, saɓanin yadda zai gamsu ko yake ganinsu a cikin ƙamus (Dictionary). Hakan kuma ya faru ne saboda a yanzu muna cikin wani zamani ne mai suna “turban masana”, ko Information Highway, kamar yadda bayani ya gabata a ƙasidar Matambayi ba ya ɓata. A wannan zamani, kalmomin harsunan duniya za su yi ta sauyawa ne iya gwargwadon fannin ilimi ko rayuwar da ake amfani da su. Don haka sai a kiyaye.
| |
Iri | invention (en) |
---|---|
Time of discovery or invention (en) | 1945 |
Has part(s) (en) | |
input-output device (en) Fasahar mashigar rubutun kwamfuta central processing unit (en) computer hardware (en) software graphics processing unit (en) |