Kasuwa
From Wikipedia, the free encyclopedia
Kasuwa, wani keɓantaccen guri ne da ake tanada don haɗuwa a yi cinikayya wato saye da sayarwa. Gurin hada-hadar kasuwanci [1] Wanda ita kasuwa tana haɗa mutane daban-daban daga wurare mabam-banta da ƙasashe daban-daban kuma ita kasuwa kusan komai akwai a cikinta. Jam'in kasuwa shi ne kasuwanni haka kuma wanda yake harkar kasuwanci ana ce masa ɗan kasuwa. Ana yi wa kasuwa kirari da "kasuwa akai maki tilas in an ƙiya a kai maki babu" kasuwanni iri-iri ne akwai kasuwar dabbobi akwai kuma kasuwar hatsi da dai sauran kasuwanni. Akwai kasuwa da ake cinikayya ta cikin ƙasa akwai kuma ta ƙasa da ƙasa.[2]
Quick Facts Bayanai, Ƙaramin ɓangare na ...
Kulle