Gazawar zuciya
From Wikipedia, the free encyclopedia
Cutar gazawar zuciya ( HF ), wanda kuma aka sani da ciwon zuciya na congestive heart failure ( CHF ), ciwo ne, rukuni na alamu da alamomin bayyanar cututtuka, wanda ya faruwa a dalilin illolin bubbugar jini daga zuciya. Alamomin cutar sun haɗa da ƙarancin numfashi, yawan gajiya, da kumburin ƙafafu. Ƙunƙarar numfashi na iya faruwa yayin aiki ko a yanayin kwanciya, kuma yana iya hana mara lafiya baci da dare . Ciwon ƙirji, gami da angina, ba yawanci ciwon zuciya ne ke haifar da shi ba, amma yana iya faruwa idan ciwon zuciya ya haifar da cutar zuciya (heart attack).[8][9] Ana gano tsananin cutar gazawar zuciya ta hanyar gwajin ejection fraction da kuma auna ta da tsananin alamominta. Sauran yanayi waɗanda zasu iya samun alamun bayyanar cututtuka irin su gazawar zuciya sun haɗa da kiba, gazawar koda, cututtukan hanta, anemia, da cutar thyroid.
Gazawar zuciya | |
---|---|
Mutum me cutar gazawar zicya ta congestive heart failure da alama ta jugular venous distension. External jugular vein wanda akayi da arrow | |
Rabe-rabe da ma'adanai da waje | |
Symptoms | daukewar numfashi, exhaustion, kumburewar kafafu[1] |
Duration | Tsawon rayuwa |
Causes | Heart attack, high blood pressure, abnormal heart rhythm, excessive alcohol use, infection, heart damage[2] |
Risks | Smoking, sedentary lifestyle, exposure to second-hand smoke[3] |
Diagnosis | Echocardiogram[4] |
Similar conditions | Kidney failure, thyroid disease, liver disease, anemia, obesity[5] |
Medication | Diuretics, cardiac medications |
Frequency | 40 million (2015),[6] |
Deaths | 35% risk of death in first year[7] |