Diana Liverman
From Wikipedia, the free encyclopedia
Diana Liverman (an haife ta a watan Mayu 15, 1954, Accra, Ghana)farfesa ce ta Regents Farfesa ta Geography da Cigaba, kuma tsohuwar Darakta ta Jami'ar Arizona School of Geography, Development and Muhalli a Kwalejin Kimiyyar Zamantakewa da Halayyar a Tucson, Arizona. Liverman tayi nazarin canjin muhalli na duniya da tasirin yanayi akan al'ummar bil'adama, gami da tasirin fari da yunwa akan al'umma, noma, tsarin abinci, da kuma jama'a masu rauni.[1]Ta damu musamman game da matakan dai-daitawa waɗanda ke magance sauyin yanayi, abin da ke sa suyi nasara, da kuma lokacin da suka ƙirƙiri ko ƙarfafa rashin daidaituwa.[2] Liverman tayi nazari akan yuwuwar rage illolin sauyin yanayi da kuma cimma burin cigaba mai dorewa na Majalisar Ɗinkin Duniya. Acikin 2010, Liverman ta karɓi lambar yabo ta Founder's Medal of the Royal Geographical Society, don "ƙarfafawa, haɓakawa da haɓɓaka fahimtar yanayin ɗan adam na canjin yanayi".
Diana Liverman | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Accra, 15 Mayu 1954 (69 shekaru) |
ƙasa |
Birtaniya Tarayyar Amurka |
Karatu | |
Makaranta |
University of Toronto (en) 1979) Master of Arts (en) : labarin ƙasa Jami'ar Kwaleji ta Landon 1976) Bachelor of Arts (en) : labarin ƙasa University of California, Los Angeles (en) 1984) Doctor of Philosophy (en) : labarin ƙasa |
Thesis director | Stephen Schneider (en) |
Harsuna | Turanci |
Sana'a | |
Sana'a | masanin yanayin ƙasa, science writer (en) da environmentalist (en) |
Employers |
University of Wisconsin–Madison (en) (1985 - 1989) Pennsylvania State University (en) (1990 - 1995) University of Arizona (en) (1996 - 2002) Environmental Change Institute (en) (2003 - 2008) University of Arizona (en) (2009 - Jami'ar Oxford (2009 - |
Kyaututtuka |
gani
|
Mamba |
American Academy of Arts and Sciences (en) National Academy of Sciences (en) British Academy (en) |
Liverman ta kasance mawallafiyar Ƙungiyar Ƙwararru(IPCC) Oktoba 8, 2018 Rahoton Musamman game da Dumamar Duniya na 1.5°C. Liverman tana ɗaya daga cikin masana kimiyya 19 a duk duniya da aka zaɓa zuwa Hukumar Duniya a 2019. Acikin 2020, an zaɓi Liverman zuwa Cibiyar Nazarin Kimiyya ta ƙasa da zuwa Cibiyar Fasaha da Kimiyya ta Amurka.