Cutar huhu
From Wikipedia, the free encyclopedia
Cututtukan numfashi, ko cututtukan huhu,[1] cututtuka ne da ke shafar gabobi da tsoka - tissue wanda ke haifar da wahalar numfashi ga dabbobi masu shakar iska. Sun hada da yanayi na cututtukan hanyoyin numfashi ciki har da trachea, bronchi, bronchioles, alveoli, pleurae, pleural cavity, jijiyoyi da gabobin numfashi. Cututtukan na numfashi sun hada da masu sauki ko wanda za'a iya shawo kansu cikin sauki, irin su mura, majina da tari, da kuma pharyngitis zuwa cututtuka masu barazana ga rayuwar dan-Adam irin su asthma da sankarar huhu, tarin fuka, asma mai tsanani, ciwon huhu,[2] da cututtuka masu tsanani na numfashi kamar COVID-19.[3] Ana iya rarraba cututtuka na numfashi ta hanyoyi daban-daban, kamar dangane da gabobin jiki ko nama da ke kamuwa da cutar, t ko kuma ta alamomin da dalilan cutar.
Respiratory disease | |
---|---|
Micrograph of an emphysematous lung; emphysema is a common respiratory disease, strongly associated with smoking. H&E stain. | |
Rabe-rabe da ma'adanai da waje |
Ana kiran karatun nazarin cututtukan da suka shafi numfashi da pulmonology. Likitan da ya kware akan cututtukan numfashi ana kiran shi da likitan huhu pulmonologist, ƙwararren likitan ƙirji, ƙwararrun likitancin numfashi, likitan numfashi ko ƙwararren likitancin thoracic.