Claude Monet
From Wikipedia, the free encyclopedia
Claude Monet (14 Nuwamban shekarar 1840 zuwa 5 Disamban shekarar 1926) mai zane ne na kasar Faransa kuma wand aya kirkiro zanen impressionism, wanda Kuma ake gani a matsayin jigo na zanukan zamani, musamman yanda yake ƙoƙarin zanen yanayi a yanda ya fahimce shi.[1] A zamanin ayyukansa masu dogon tarihi, shine mafi shahara da kwarewa a salo zanen impressionism - wato falsafar zane ta hanyar fahimtar shi mai zanen ga wuri ko yanayi musamman zanen sarari (waje) da kuma yanayi ƙasa wato landscape.[2] Kalmar "Impressionism" wato ra'ayin mai zane, ya samo asali ne daga zanensa mai suna Impression, Sunrise wanda aka gabatar a 1874 a wajen taron baje koli na Salon.
Claude Monet | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | Oscar-Claude Monet |
Haihuwa | Faris, 14 Nuwamba, 1840 |
ƙasa | Faransa |
Mazauni |
Giverny (en) Villa Saint-Louis (en) Argenteuil (en) Vétheuil (en) |
Mutuwa | Giverny (en) , 5 Disamba 1926 |
Makwanci | Giverny Churchyard (en) |
Yanayin mutuwa | Sababi na ainihi (Ciwon huhun daji) |
Ƴan uwa | |
Abokiyar zama |
Camille Doncieux (en) (28 ga Yuni, 1870 - 5 Satumba 1879) Alice Hoschedé (en) (16 ga Yuli, 1892 - 19 Mayu 1911) |
Yara | |
Ahali | Léon Monet (en) |
Karatu | |
Makaranta | Beaux-Arts de Paris (en) : Painting |
Harsuna | Faransanci |
Malamai | Marc-Charles-Gabriel Gleyre (en) |
Ɗalibai | |
Sana'a | |
Sana'a | painter (en) da mai zane-zanen hoto |
Wurin aiki | Faris, Argenteuil (en) , Vétheuil (en) , Poissy (en) , Giverny (en) , Honfleur (en) , Trouville (en) , Amsterdam, Oegstgeest (en) , Sassenheim (en) , The Hague (en) , Zaandam (en) da Landan |
Muhimman ayyuka |
Zanen Ra'ayi, fitowar rana Garden at Sainte-Adresse (en) Houses of Parliament serie (en) La Corniche near Monaco (en) Water Lilies (en) Rouen Cathedral Series (en) |
Wanda ya ja hankalinsa | Gustave Courbet (en) , Jean-François Millet (en) , Édouard Manet (en) , J. M. W. Turner (en) da Hokusai |
Fafutuka | Zanen Ra'ayi |
Artistic movement |
landscape art (en) still life (en) Hoto (Portrait) |
IMDb | nm1217328 |
Monet ya girma ne a garin Le Havre, Normandy, kuma ya fara sha'awar zanen waje tun daga ƙananun shekarunsa. Duk da cewa mahaifiyarsa Louise-Justine Aubrée Monet ta mara masa baya don cika burinsa na zama mai zane, mahifaisa kuwa wato Claude-Adolphe bai amince da hakan ba inda yake so ya zama dan kasuwa. Yana da kyakyawar alaka da mahaifiyarsa sai dai ta mutu ne a cikin watan Junairun shekarar 1857, a lokacin yana da shekaru goma sha shida a duniya, sannan aka turashi don yayi rayuwa a karkashin kulawar goggonsa attajira wacce bata taba haihuwa ba, Marie-Jeanne Lecadre. Daga nan ya zarce don yin karatu a jamiar Académie Suisse, kuma yayi karatu a karkashin shahararren masanin tarihin zane Charles Gleyre, kuma ya zamo abokin karatu ga Auguste Renoir. Ayyukansa na farko-farko sun hada da yanayin kasa, sassan teku, da zanen mutane wanda amma basu samu karbuwa ba da farko. Wani muhimmin mutum a rayuwar sana'arsa shine Eugène Boudin wanda ya koya masa salon zanen yanayi. Tun daga 1883, Monet ya cigaba da rayuwa a garin Giverny, wanda ke arewacin Faransa, inda ya siya gida da kuma fili kuma ya fara manyan ayyukan zanen filaye wanda suka hada da zanen korama na water-lily.
Burin Monet na ajiye kundin zanen yankunan Faransa ya kawo wani sabon salo na zane wanda ke daukar lokutan yini daban daban da kuma wucewar yanayi. Daga cikin wadannan zanuka na musamman da sukayi fice sun hada da zanen haystacks (1890–91), zanen Rouen Cathedral(1894), da kuma zanensa na Water lillies wanda ya kwashe tsawon shekaru ashiri yana yi.
Monet ya kara shahara da fice a cikin karni na 20, lokacin da ya zamo daya daga cikin muhimman masu zane na duniya kuma abun kwaikwayo ga sauran ƙungiyoyin masu zane da ke tasowa.