Ba wa Juna Tazara
From Wikipedia, the free encyclopedia
A ƙarnin da ya wuce, annoba iri - iri masu alaƙa da mashaƙo sun bijiro sun gallabi duniya. Waɗannan annoba suna da titstsige daga ƙwayoyin cututtuka da ke jikin dabbobi da tsuntsaye, akan samu wani lokaci suna shiga jikin ɗan adam suna haddasa masa ciwo. Daga nan kuma sai su cigaba da yaɗuwa daga mutum zuwa mutum.[1] Ana kiransu 'zoonotic' cikin harshen Ingilishi saboda cututtukan sun samo asali ne daga dabbobi.
An taskan ce wannan muƙalar a cikin jerin Muƙaloli_masu_kyau a Hausa Wikipedia
Ana sa ran wata rana wannan muƙalar zata kasance a Babban Shafin Muƙalar mu a yau |
Ba wa Juna Tazara | |
---|---|
social behavior (en) da activity policy (en) | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | non-pharmaceutical countermeasure (en) |
Bangare na | infection control (en) |
Has goal (en) | minimization (en) |
Hashtag (en) | SocialDistancing |
Yin tazara da juna shi ne ɗaya daga manyan hanyoyin daƙile yaɗuwar irin waɗannan cututtuka musamman Kwabid-19. Ba wa juna tazara na nufin nisantar gwamutsuwa da juna ta yadda za a samu sasari tsakanin al'umma ba tare da cakuɗuwa ba.[2] Dakta Jeff Kwong, wanda yake ƙwararre ne a fannin nazarin cututtuka masu yaɗuwa na Jami'ar Toronto, ya bayyana ma'anar ba da tazara akan cewa dukkan abubuwan da mutane za su aikata domin daƙile yaɗuwar cututtuka tsakaninsu. Wannan kuwa ya haɗa har da zaman killace kai. Domin mu fahimci yadda ba wa juna tazara ke gudana, za mu yi la'akari da wani tsarin da ƙwararru a fannin cututtuka masu yaɗuwa suka samar. Bari mu ɗauki wannan tsari bisa la'akari da annobar Kwabid-19 ta shekara 2019/2020 da bayanan da aka samu daga kasar China inda cutar ta fara sannan za mu duba yadda tsarin yake a ƙasar Afrika ta Kudu. Wannan kuma zai ba mu damar mu dubi irin tasirin da ba wa juna tazara ke da shi wajen daƙile yaɗuwar cutar Kwabid-19.[3] A ƙarshen wannan muƙala mun yi duba da yadda za a magance matsalolin da zaman tazara ka iya haifarwa.