Ahmed Musa
Dan Wasan kungiyar Kwallon Kafa ta Najeriya / From Wikipedia, the free encyclopedia
Ahmed MusaAhmed Musa (Taimako·bayani) (an haife shi a ranar goma sha hudu (14) ga watan Oktoba (10), shekara ta alib dubu daya da dari tara da cassa'in da biyu "1992") ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na Najeriya wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan gaba da hagu zuwa ƙungiyar Süper Lig ta Turkiyya Fatih Karagümrük da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Najeriya.
Ahmed Musa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Jos, 14 Oktoba 1992 (31 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harshen uwa | Hausa | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Mahalarcin
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa |
Mai buga tsakiya wing half (en) Ataka | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Lamban wasa | 18 | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Nauyi | 62 kg | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 170 cm | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Imani | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Addini | Musulunci |
Musa ya zama dan Najeriya na farko da ya ci fiye da sau daya a gasar cin kofin duniya ta FIFA, bayan da ya ci Argentina kwallaye biyu a gasar cin kofin duniya ta shekara dubu biyu da goma sha huɗu (2014). Musa shi ne dan Najeriya na farko da ya zura kwallo a gasar cin kofin duniya ta FIFA guda biyu, bayan ya zura kwallaye biyu a ragar Iceland a matakin rukuni na gasar cin kofin duniya ta FIFA 2018. Musa ya kasance memba na kungiyar Al Nassr da ta lashe gasar Premier ta Saudiyya da kuma Super Cup na Saudiyya, duka a shekara ta dubu biyu da goma sha tara (2019).[1]