Afirka ta Yamma
From Wikipedia, the free encyclopedia
Afirka ta Yamma ko Yammacin Afirka ita ce yammacin nahiyar Afirka. Majalisan Dinkin Duniya sun bayyana Yammacin Afirka a matsayin ƙasashe Goma sha shida 16, sune Benin, Burkina Faso, Cape Verde, Gambia, Gana, Gini, Guinea-Bissau, Côte d'Ivoire, Liberia, Mali, Muritaniya, Nijar, Najeriya, Senegal, Sierra Leone da kuma Togo, haka kuma harda wasu tsuburi.[1] Yawan ƴan Yammacin Afirka sun kai kimanin, Mutane 381,981,000 a ƙidayar shekara ta 2017, Mata sun kai kimanin 189,672,000, Maza kuma 192,309,000.[2] Shekarunta da yaɗuwarta da kuma bambance-bambance a duk faɗin Nahiyar ta sa ainihin ma'anarta a cikin Afirka,[3] [4] [5] [6] [7] san nan kuma akwai yaruka masu yawa awanan kasashen ta Afrika tayamma.