Hanyoyin gano ƙwayar cuta
From Wikipedia, the free encyclopedia
Hanyoyin gano kwayar cuta a harkar kiwon lafiya, wata hanya ce da ake bi don gano asalin kwayar cuta, ko kuma wani yanayi ne da alamomi ke bayyana yayin da gwaji ya tabbatar. Sau da yawa gane asalin kwayar cuta ta hanyar gwaje-gwajen likitoci.
Hanyoyin gano kwayar cuta |
---|
Abubuwan da ake bukata wajen gano asalin kwayar cuta, sun hadar da tarihi ko abinda ya bayyana na rashin lafiyar majinyacin, da kuma gwaje-gwajen likitoci a kan wanda ake kokarin bawa kulawa.
Hanyoyin gwajin sune; daukar samfuri, wasu lokutan bincike kan gawar mamaci a kanyi la’akari da shi wajen gano asalin kwayar cutar da ta same shi.
Sau da yawa ana kuma fuskantar kalubale saboda mafi yawan alamun cututtuka na wahalar ganewa musamman yadda suke kamanceceniya da wasu.
Misali sauyawar launin fata zuwa ja, yakan iya zama alamar cututtuka da dama, dan haka kwararru basa iya gane takamaiman matsalar (gwajine kawai zai tabbatar).