Antarah ibn Shaddad
From Wikipedia, the free encyclopedia
ANTARAH IBN SHADDAD AL-ABSYAfarkon rayuwarshi anfi kiranshi da "Antarah bin Zhabibah" Amman daga karshen rayuwarshi ya shahara da "Antarah bin Shaddad" ( Larabci: عنترة بن شداد العبسي , Labarin AntaAntrah ibn Shadād al-ʿAbsī ; AD 525–608), , ya kasance daya daga cikin shararrun labaran soyayya masu cike da al'ajabi dasuka faru ayankin larabawa bayan Labarin Lailah Majnoon Antarah yakasance dane ga wata baiwa me suna Zhabibah yatashi cikin tsangwama da tsana daga kabilar Absi sakamakon kasancewar mahaifiyarshi bakar fata daga Afrika kuma Baiwa sakamakon tsanar da akemishi hartakai Mahaifinshi Shaddad bayason andaganta Antarah dashi saboda tsabar nunu wariyar launi.Bayan gwagwarmaya dayasha Akan soyayyar Wata yar yayan Mahaifinshi Ablah bint Malek Antarah yakasance jarumi,kuma fitaccen mawaƙin Larabawa kafin Jahiliyya, ya shahara ga duka waƙoƙinsa da rayuwarsa mai jan hankali. Babban waƙarsa tana cikin jerin Mu'allaƙāt, tarin '' ƙamshi mai rataye '' bakwai da aka ce an dakatar da su a cikin Ka'aba . Antarah yafara soyayyar Ablah tun yana matashi kaskantacce acikin kabilarsu Ablah Bani Absi mahaifiyarshi kanta bata goyi bayan wannan soyayya ba saboda tasan Bani Absi bazasu taba bada Auren kyakkywar mace irin Ablah ga Bakin Bawa ba, Amman ahaka Antarah yayita Neman haryar dazai gabatar da soyayyarshi ga Ablah bint Malek Amman yanajin shakkar cin mutunchin dazai fuskanta daga iyayenta. Kwatsam! Wata rana aka kawo farmaki akan kabilar Bani Absi gashi kuma Babban Ablah Malek da wasu mayakan kabilar duk basanan,Awannan rana ne jarumtar Antarah tafito fili saboda yanda yayi yaki da jarumta kuma yakwato masu matan Bani Absi da akafara kamawa amatsayin ribatattun yaki ciki kuwa hada Ablah Bint Malek,bayan Baban Ablah yadawo sukaji labarin jarumatar da Antarah yayi hakan tasa aka karramashi akamishi kyaututtuka nagirma kuma akafara dangantashi da Mahaifinshi wartou Antarah Ibn Shaddad daga wannan lokaci kuma yasamu damar nuna soyayyarshi ga Ablah afili kodayake duk dahaka Mahaifinta bayason yabada Aurenta ga Antarah,Malek yafison yabawa wani Baban attajiri Dan Kabilar Bani Absi. Lissafin rayuwarsa ya zama tushen dogon soyayya da saida rai tare da juriya a Soyayya.
Antarah ibn Shaddad | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Najd (en) , 525 |
Mutuwa | Ḥaʼil Province (en) , 608 |
Yanayin mutuwa | kisan kai |
Ƴan uwa | |
Ahali | Shayboub ibn zabiba (en) |
Karatu | |
Harsuna | Larabci |
Sana'a | |
Sana'a | maiwaƙe da marubuci |